Man Utd za ta sayar da Pogba, Chelsea na iya korar Lampard

Paul Pogba

Asalin hoton, PA Media

Akwai yiwuwar dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba zai bar Manchester United a wannan bazara amma kulob din ya ce yana son sama da fam miliyan £150 kan dan wasan mai shekara 26. (ESPN)

Wakilin Pogba, Mino Raiola, ya ce ya cimma yarjejeniya da kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer bayan tafka muhawara. (Sky Sports)

Dan uwan Pogba, Mathias, ya ce "kowa ya sani yana son barin" Manchester United domin ya buka gasar Zakarun Turai saboda yana son lashe kofuna. (Sun)

Manchester City na son dan wasan Bayern Munich Serge Gnabry, mai shekara 24, a madadin dan wasanta Leroy Sane, mai shekara 24. (Sun)

KocinChelsea Frank Lampard na fuskantar barazanar kora idan har ya kasa samar wa kungiyar gurbin zuwa gasar zakarun Turai. (Telegraph)

Manchester United na tunanin dauke daraktan wasanni na Paris St-Germain Antero Henrique da kuma shugaban wasanni na Red Bull a matsayin babban mai bayar da horo. (Independent)

Dan wasanRB Leipzig na Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 21, ya ce ya san kungiyoyi kamar Barcelona da Arsenal na ra'yinsa. (RMC Sport, via Goal)

Chelsea na sa ido kan matashin dan wasan tsakiya na Birmingham City mai shekara 16 Jude Bellingham, amma Manchester United da Barcelona da Real Madrid sun nuna sha'awar dan wasan. (Goal)

Barcelona na son dauko dan wasan gaba na Leganes Martin Braithwaite, mai shekara 28, domin maye gurbin dan wasanta na Faransa Ousmane Dembele, mai shekra 22 da ke jinyar rauni bayan ta hakura da dan wasan Real Sociedadna Brazil, Willian Jose, mai shekara 28. (Sky Sports)

Kamfanin Puma da yi wa Manchester City tufafi yana fatan kulob din zai yi nasara kan haramcin shekara biyu na buga wasannin gasar Turai tsawon shekara biyu. (Telegraph)

Dan wasan baya Giorgio Chiellini, mai shekara 35, zai tsawaita kwantaraginsa a Juventus zuwa watanni 12. (Goal)