Reinier ya sharbi kuka a gaban magoya Real Madrid

Asalin hoton, Reuters
Matashin dan wasa, Reinier Jesus ya sharbi kuka a gaban magoya bayan Real Madrid a lokacin da aka gabatar da shi ranar Talata.
Dan wasan mai shekara 18, ya ce mafarkinsa ne tun yana yaro ya zama gaskiya da ya zama dan kwallon Real Madrid, dalilin da ya sa ya yi kukan murna kenan.
Matashin dan kwallon ya koma Spaniya da taka leda daga Flamengo kan fam miliyan 26 a watan Janairu.
Reinier ya ce ''Yana kishirwar zama cikin wadan da suka kafa tarihi a Real Madrid''.
''Wannan rana ce mai dumbin tarihi da ba zan manta da ita ba'',
reiner yana cikin 'yan kwallon tawagar Brazil da suka lashe Copa Libertadores a bara, ya kuma je gasar Zakarun nahiyoyin duniya, amma bai buga karawa da Liverpool ba.