Borrusia Dortmund ta mallaki Emre Can

emre Can

Asalin hoton, Getty Images

Emre Can ya zama dan kwallon Borussia Dortmund - kwana 18 da komawarsa Jamus, domin buga wasannin aro daga Juventus.

Dan kasar Jamus, mai shekara 26, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara hudu kan fam miliyan 21.

Kawo yanzu ya buga wa Dortmund wasa uku, ya kuma ci kwallo a ranar da ya fara buga mata tamaula.

Tsohon dan kwallon Liverpool, ya buga wasa biyu kacal a Serie A, tun bayan da Maurizio Sarri ya karbi aikin horas da Juventus a bara.

Dan wasan ya koma Juventus daga Liverpool a watan Yunin 2018, lokacin da kwantiraginsa ya kare a Anfield.

Dan kwallon ya kuma buga wa Bayern da kuma Bayern Leverkusen tamaula.

Dortmund ce ta yi ta biyu a bara a gasar Bundesliga, yanzu kuma tana ta biyu a kan teburin bana da tazarar maki hudu tsakaninta da Bayern Munich ta daya.