An ci Liverpool da PSG a Champions League

Atletico

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta yi rashin nasara da ci 1-0 a Atletico Madrid a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai da sukka fafata ranar Talata.

Atleticon ta ci kwallon ne a minti hudu da fara wasa ta hannun Saul Niguez.

Karon farko kenan da Liverpool ta yi rashin nasara a champions League a bana, bayan 2-0 da Napoli ta doke ta ranar 17 ga watan Satumbar 2019 a Italiya.

Liverpool tana ta daya a teburin Premier da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Kungiyar ta Anfield za ta karbi bakuncin Atletico a wasa na biyu ranar 11 ga watan Maris.

Asalin hoton, Getty Images

Ita kuwa Borussia Dortmund ta yi nasara ne a kan Paris St-Germain da ci 2-1 a karawar da suka yi a Jamus.

Kungiyoyin sun buga minti 45 babu ci, illa hare-hare da suka dunga kai wa junansu.

Sai bayan da suka koma zagaye na biyu ne Dortmund ta ci kwallo ta hannun Erling Haaland daga baya minti shida tsakani Neymar Da Silva ya farke.

Daga baya ne Dortmund ta kara na biyu ta hannun Erling Haaland wanda ya ci biyu a karawar.

Dortmund za ta ziyarci Paris St Germain a wasa na biyu na Champions League ranar 11 ga watan Maris.