Liverpool ta bukaci Lallana ya nemi wata kungiyar

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta amince wa Adam Lallana da ya nemi wata kungiyar a karshen kakar bana, bayan da kwantiransa zai kare.

Kungiyar ba ta tattauna da dan kwallon tawagar Ingila ba don sabunta yarjejeniyarsa, saboda haka zai iya komawa wata kungiyar kenan a karshen kakar shekarar nan.

Lallana wanda ake alakanta shi da zai koma Leicester City da murza leda, ya koma Anfield a shekarar 2014 kan fam miliyan 25.

Ya koma Liverpool ne daga Southampton a lokacin koci Brendan Rodgers, wanda yanzu ke horas da Leicester City.

Dan wasa ya buga wa Liverpool karawa 13 a gasar Premier ya kuma ci mata kwallo daya tal.

Lallana ya yi fama da jinya a kaka biyu da ta wuce, sai dai yana daga cikin 'yan wasan da Jurgen Klopp ya yi amfani da shi a farkon zuwansa Anfield da horas da tamaula.