Cazorla na fatan kasaitaccen ban kwana a Arsenal

Carzola

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon dan wasan Arsenal, Santi Cazorla ya ce zuwa yin ban kwana a Gunners shi ne abin da ya rage masa a harkar kwallon kafarsa.

Cazorla. mai shekara 35, ya bar Emirates a shekarar 2018, bayan shekara shida da ya yi a kungiyar.

Dan wasan ya koma Villareal da murza leda har ya zama kashin bayan kungiyar, ya kuma shiga cikin tawagar 'yan kwallon Spaniya.

Carzola ya shaidawa BBC cewar ''Abin bakin ciki ne da na bar Arsenal ba tare da yin ban kwana ba da kungiyar da ta yi min komai a rayuwa''.

''Abin da ya rage min kenan a harkar kwallon kafa, na yi ban kwana kamar yadda ya dace. Ina jinjina ga kungiyar da magoya bayanta kan yadda suka maramin baya''.

Wasu rahotanni na cewar Gunners na shirin bai wa Carzola aiki nan gaba, sai dai dan wasan ya ce bai da shirin yin aikin koci da Mikel Arteta kawo yanzu da saura.

Carzola ya taka leda tare da Arteta a Arsenal ya kuma ce kungiyar ta samu kocin da ya dace da ita.