Klopp ya gargadi Atletico zuwanta Anfield

Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

Jurgen Klopp ya ja kunnen Atletico Madrid cewar su kwan da sanin magoya bayan Liverpool za su marawa kungiyarsu baya dari bisa dari idan suka je Anfield.

Atletico Madrid ta yi nasarar cin Liverpool 1-0 a wasan farko na zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions Leagues da suka fafata ranar Laraba.

Minti hudu da fara wasa Saul Niguez ya ci Liverpool mai rike da kofi, kuma haka aka tashi wasan ba ta farke ba.

Magoya bayan Atletico sun marawa kungiyarsu baya da kara kwarin gwiwa kamar yadda koci Diego Simeone ya dunga bukatarsu.

Klopp ya ce 'Ina yi wa magoya bayan Atletico wadan da za su sayi tikiti da lale da zuwa Anfield''.

''Klopp ya ce marawa kungiya baya wani abu ne mai mahimmaci kamar yadda 'yan atletico suka dunga rera wakar yabo ga 'yan wasa.

''Yanzu dai an buga wasan farko za kuma a karkare a Anfield, saboda haka su kwan da sanin yadda magoya bayan Liverpool za su kara musu kwarin gwiwa tun fara wasa har kammala shi.

Atletico Madrid za ta ziyarci Liverpool a wasa na biyu ranar 11 ga watan Maris.

Tuni Liverpool ta samu tikitin buga Champions League na badi, bayan da take ta daya a teburin Premier da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City ta biyu.