Rondon na son komawa Man Utd, LA Galaxy ta tuntubi Messi

Salomon Rondon

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon dan wasan Newcastle da West Brom dan kasar Venezuela Salomon Rondon, mai shekara 30, ya yi amannar cewa Manchester United ta yi jinkiri a yunkurinta na sayo shi daga kulob din Dalian Professional da ke buga gasar League ta kasar China. (AS, via Star)

Manchester United na da kwarin gwiwar sayen dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 19, a bazara mai zuwa, amma dole sai sun cancanci buga gasar Zakarun Turai. (Sky Sports)

Dan wasan RB Leipzig Timo Werner, mai shekara 23, ya ce yana "alfahari" da aka alakanta shi da yunkurin komawa Liverpool ko da yake ya kara da cewa yana jin bai shirya komawa kungiyar da yake gani a matsayin "mafi inganci a duniya" ba. (Metro)

Kungiyar LA Galaxy ta yi wayar tarho da dan wasan Barcelona da Argentina Lionel Messi, mai shekara 32, domin yiwuwar komawarsa. (Express)

Messi ya amince cewa wasu abubuwa na "ba-sa-ban ba" suna faruwa a Barcelona a yayin da rahotanni ke cewa kungiyar ta dauki hayar kamfanin shafukan sada zumunta domin ya rika caccakar 'yan wasanta. (Mundo Deportivo, via Mail)

Messi ya ce yana daukar Barcelona a matsayin "gidansa" a yayin da ake rade radin cewa zai iya barin Nou Camp. (ESPN)

Juventus na son sayen dan wasan Manchester City mai shekara 22 dan kasar Brazil, Gabriel Jesus da dan wasan Paris St-Germain mai shekara 27 dan kasar Argentina Mauro Icardi a lokacin musayar 'yan kwallon kafa a bazara mai zuwa. (Tuttosport - in Italian)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kudin da Manchester United ke son Juventus ta ba ta a kan dan wasa Paul Pogba, mai shekara 26, na nufin Juve za ta auna ta gani ko kawai ta sayo dan wasan Bayern Munich da Spain Thiago Alcantara, mai shekara 28, mai makon Pogba. (Tuttosport, via Mail)

Liverpool na shirin sayo dan wasan Werder Bremen da Kosovo, Milot Rashica, mai shekara 23, wanda za a sayar da shi a kan £31.5m. (Bild, via Mirror)

Chelsea na matukar sha'awar sayo dan wasan Birmingham City, Jude Bellingham, mai shekara 16, amma farashin £50m da aka sanya a kan dan wasansu mai shekara 18 Faustino Anjorin zai iya shafar zamansa na dogon zango a kungiyar. (Sun)

Dan wasan Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, zai yi bakin kokarinsa a Chelsea nan da watanni kadan masu zuwa duk da cewa bai samu damar barin kungiyar ba lokacin musayar 'yan kwallo a watan Janairu domin komawa Stamford Bridge. (Mirror)

Arsenal na burin sayo dan wasan Bayer Leverkusen dan kasar Jamus Jonathan Tah, mai shekara 24, wanda za a sayar a kan euro 40m a bazara. (Bild - in German)

Arsenal, Everton da kuma Leicester City na cikin kungiyoyi bakwai da ke sha'awar sayo dan wasan Gent da Canada Jonathan David, mai shekara 20. (Jeunes Footeux, via Sun)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya amince cewa ya ki sanya Matteo Guendouzi, mai shekara 20, a wasan da suka doke Newcastle ne saboda rashin da'ar da dan wasan ya nuna lokacin da suka je Dubai domin yin atisayen hutun rabin wasannin gasar Firimiya. (Mirror)