Rangers ta ci Pillars a kwantan gasar Firimiya

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto NPFL

Rangers International ta yi nasarar doke Kano Pillars da ci 1-0 a kwantan gasar Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Laraba.

Rangers ta ci kwallon ne ta hannun Chinonso Eziekwe saura minti 25 a tashi daga karawar.

Da wannan sakamakon Rangers ta hada maki 23 a wasa 17 da ta buga, ita kuwa Pillars tana nan da makinta 27 da kwantai daya.

Daya kwantan wasan kuwa, Enyimba International ta doke Kwara United da ci 2-0.

Wikki ta ragargaji Lobi Stars da ruwan kwallaye

MFM ta taka wa Kano Pillars burki a gasar Firimiya

An kammala zangon farko a gasar Firimiyar Najeriya

Enyimba ta ci kwallon farko ta hannun Stanley Dimgba minti biyar da fara wasa, sannan Victor Mbaoma ya kara na biyu saura minti biyar a tashi daga gumurzun.

Enyimba ta hada maki 30 kenan, bayan wasa 17, ita kuwa Kwara tana da makinta 24.

Rangers da Enyimba na buga gasar zakarun Afirka ta Confederation Cup, dalilin da suka tara kwantan wasanni kenan.

A ranar Lahadi aka kammala wasannin farko a zango na biyu, inda Plateau United ta dare mataki na daya, Lobi ta koma ta biyu a teburi, bayan wasa 20.

Ranar 23 ga watan Fabrairu za a ci gaba da wasannin mako na 21

Labarai masu alaka