Morocco na zawarcin wasan karshe a Zakarun Afirka

CAF Leagues

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafar Morocco ta mika bukatar son karbar bakuncin wasan karshe a gasar Zakarun Afirka ta Champions League da ta Confederation Cup.

BBC ta fahimci cewar Morocco na son a buga wasan karshe a Champions League a katafaren filin wasa na Mohammed na biyar da ke Casablanca.

Ya yin da take fatan a buga wasan karshe a Confederation Cup a filin wasa na Moulay Abdellah da ke Rabat.

Tuni hukumar kwallon kafar Morocco ta aike da wasika ga hukumar kwallon kafar Afirka, CAF, kan bukatar izinin karbar bakuncin wasannin.

Hakan ya biyo bayan da CAF, ta umarci dukkan mambobinta da suke da sha'awar karbar bakuncin wasannin da su yi zawarci, ita kuma ta zabi wadda za ta fitar da ita kunya.

An kuma tsayar da ranar Alhamis 20 ga watan Fabrairu domin rufe karbar takardun zawarcin wasannin na Zakarun Afirkan.

Morocco ce ta biyu da ta nuna bukatar hakan, bayan Afirka ta Kudu da za a yi wasan karshe a Champions League 29 ga watan Mayu, a yi na Confederation 24 ga watan Mayun.