Man City ta rage tazara tsakaninta da Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta yi nasarar doke West Ham United da ci 2-0 a kwantan wasan mako na 26 da suka kara a Etihad.
Tun farko karawar ta zama kwantai bayan da rashin kyawun yanayi ya sa aka dage fafatawar ta su.
City ta fara cin kwallo ne ta hannun Rodri saura minti 15 a je hutun, bayan hutun ne City ta kara na biyu ya hannun Kevin de Bruyne.
Karo na uku kenan Rodri na ci wa City kwallo kuma na farko a filin wasa na Etihad.
Kuma kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa aka ci kwallo tara da ka a tarihin Premier bana, sai West Ham mai guda takwas.
Da wannan sakamakon City ta rage tazarar maki da ke tsakaninta da Liverpool ta daya a teburi daga 25 yanzu ya koma 22.
West Ham tana nan a mataki na 18 da maki 24, bayan buga wasan Premier 26.
Asalin hoton, BBC Sport
City za ta ziyarci Leicester City a wasan mako na 27 a gasar ta Premier ranar 22 ga watan Fabrairu.
Ita kuwa West Ham United za ta ziyarci Liverpool ne ranar Litinin 24 ga watan Fabrairu.