An jefa Tottenham a matsi a Champions League

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham ta yi rashin nasara a hannun RB Leipzig da ci 1-0 a wasan farko na zagaye na biyu a Champions League da suka kara Laraba.

Kungiyar Jamus ta yi nasarar cin kwallo ne a zagaye na biyu a bugun fenariti ta hannun Timo Werner kuma a Ingila.

Tottenham za ta ziyarci RB Leipzig domin buga wasa na biyu ranar 10 ga watan Maris.

Kafin lokacin Tottenham wadda take ta biyar a teburin Premier za ta ziyarci Chelsea ta hudu ranar 22 ga watan Fabrairu, domin buga gasar mako na 27 a Premier.

Ita kuwea Valencia ta yi rashin nasara ne da ci 4-1 a gidan Atalanta.

Atalanta ce ta fara cin kwallaye hudu ta hannun Hans Hateboer da Josip Ilicic da Remo Freuler da kuma Hans Hateboer.

Valencia ta zare kwallo daya ne ta hannun Denis Cheryshev.

A ranar 10 ga watan Maris Valencia za ta karbi bakuncin Atalata a wasa na biyu a Spaniya.