Guardiola zai ci gaba da zama a Man City

Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Pep Guardiola ya ce zai ci gaba da jan ragamar Manchester City, ya kuma ce gaskiya za ta yi halainta, bayan da UEFA ta dakatar da su.

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA ce ta dakatar da City daga shiga Champions League kaka biyu da biyan tarar fam miliyan 25.

City ta cce za ta daukaka kara kan hukuncin na UEFA a kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya.

''Mun daukaka kara. Duk wanda ya san yana da gaskiya dole ne ya fayyace kansa,'' in ji Guardiola.

''Mu kwararrun 'yan wasan kwallo ne a cikin fili, amma abin da ya faru a bayan fili babu abin da za mu iya yi.''

''Mun kuma tattauna kan abin da ya kamata muyi bayan kammala kakar tamaula ta bana, musamman kan magoya baya da ke kaunar mu.

''Za mu ci gaba da taka leda kamar yadda muka sabo, domin fitar da magoya bayan mu kunya.''

A ranar Alhamis dan kwallon City, Aymeric Laporte ya ce ;yan wasa ba sa tunanin dakatar da su da UEFA ta yi.