Klopp ya fusata 'yan wasan Madrid, Willian ba ya son barin Chelsea

Eriksen na Inter

Asalin hoton, Getty Images

'Yan wasan Atletico Madrid sun fusata sosai kuma sun yi matukar mamaki bisa korafin da kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi bayan sun doke Liverpool da ci 1-0 a zagayen farko na wasan Zakarun Turai na kungiyoyi 16, inda suka yi kira ga kocin ya mayar da hankali wurin warware matsalolin da ke damun tawagarsa. . (ESPN)

Manchester City da Barcelona za su biya karin euro 90m kan dan wasan Inter Milan dan kasar Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25, a bazara mai zuwa. (Calciomercato)

Arsenal na duba yiwuwar sayen dan wasan Bayer Leverkusen dan kasar Jamus Jonathan Tah a kan £34m. (Bild - in German)

Har yanzu Inter Milan na son sayo Marcos Alonso amma Chelsea na shirin tsuga farashi kan dan wasan mai shekara 29. (Calicomercato - in Italian)

Shugaban Crystal Palace Steve Parish ya ce yana da kwarin gwiwa kocin kungiyar Roy Hodgson zai ci gaba da aiki da su idan aka sabunta kwantaraginsa. (Sky Sports)

Dan Chelsea dan kasar Brazil Willian, mai shekara 31, wanda kwantaraginsa zai kare a kakar wasan da muke ciki, ya ce ba shi da niyyar dauke iyalinsa daga gidansu da ke London.(Mail)

A shirye Inter take ta bai wa Verona wasu 'yan wasanta a wani bangare na yarjejeniyar da za su kulla domin karbar dan wasan Albania Marash Kumbulla, mai shekara 20, wanda ake rade radin zai koma Liverpool. (Inside Futbol)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya so sayo Christian Eriksen kafin dan wasan mai shekara 28, dan kasar Denmark ya bar Tottenham zuwa Inter Milan watan jiya. (Manchester Evening News)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kungiyar Leganes ta yi mamakin yadda aka ba Barcelona damar karbo dan wasan gabanta na Denmark Martin Braithwaite, mai shekara 28, duk da an rufe kasuwar sayen 'yan wasa, inda take fatan za ta samu irin wannan damar domin sayo wani dan wasan gaba. (AS)

Juventus da Inter na son hamayya kan dan wasan Chelsea Emerson Palmieri amma kuma har yanzu ba su taya dan wasan ba mai shekara 25. (Goal.com)

Real Madrid na sa ido kan matashin da wasan tsakiya na Rennes Eduardo Camavinga, mai shekara 17. (Marca)

An bayyana cewa Manchester United na son sayen dan wasan West Ham na tsakiya Kai Corbett, mai shekara17. (Bristol Post)

Golan Bayern Munich Christian Fruchtl, mai shekara 20, ya ce ya yi watsi da tayin da Liverpool ta yi akansa a bara saboda ba ya son dumama benci. (Sport1, via Mirror)

Tsohon wasan Manchester United Robin van Persie ya ce Solskjaer na bukatar ya lashe kofin Europa League idan har yana son rufe bakin masu hamayya da shi. (Sun)

Dan wasan baya na Brazil David Luiz, mai shekara 32, ya yi imanin cewa Arsenal za ta iya daukar kofin Europa League a bana duk da ta fuskanci kalubale a bara. (Evening Standard)