Ina farin cikin kasancewa a Manchester City - Raheem Sterling

Raheem Sterling playing for Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Raheem Sterling ya koma Manchester City daga Liverpool a kan £44m a shekarar 2015

Raheem Sterling ya ce Real Madrid kulob ne mai matukar kyawu amma ya dage cewa yana cike da farin ciki a zaman da yake a Manchester City.

Ana rade radin Sterling, mai shekara 25, zai koma Real bayan da aka haramata wa City buga Gasar Turai tsawon kakar wasa biyu.

"A halin yanzu ina City kuma ina cike da farin ciki. Sai dai zan iya cewa Real Madrid kulob ne mai matukar kyawu," in ji Sterling a hirarsa da kafar watsa labaran Spain AS.

"Idan ka gan su sanye da farar taguwarsu ka san abin da kulob din ke nufi, yana da ban sha'awa."

Dan wasan na Ingila ya kara da cewa: "A lokaci daya kuma, ina da kwantaragin da yanzu na sanya wa hannu a City kuma bai kamata na yi musu butulci ba. Amma gaskiya waccan kungiyar tana da kyau."

City za ta fafata da Real Madrid a wasan 'yan rukunin 16 na gasar Zakarun Turai, inda za su yi wasan farko a Bernabeu ranar Laraba sannan su sake karawa a Etihad Stadium ranar 17 ga watan Maris.

Sau 13 Madrid suna lashe kofin, ciki har da sau uku a jere a lokacin da Zinedine Zidane yake jagorancinsu tsakanin 2016 da 2018.

A yayin da yake tsokaci a kan Zidane, wanda ya bar Real jim kadan bayan bayan sun lashe kofin karo na uku a 2018 kafin ya sake komowa Bernabeu a watan Maris, Sterling ya ce "Ina ganin lashe kofin Zakarun Turai sau da dama kuma a jere abu ne mai matukar wahala."

"Ba na tsammanin sa'a ce kawai. Tabbas sun zage dantse sun yi aiki tukuru. wasu mutane na da tunani irin na yin nasara, kuma ma ai yana [Zidane] yin nasarar."