Kante zai yi jinyar mako uku

Mason Mount ya maye gurbin N'Golo Kante jim kadan bayan fara wasansu da Manchester United

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Mason Mount ya maye gurbin N'Golo Kante jim kadan bayan fara wasansu da Manchester United

Mai yiwuwa dan wasan tsakiya na Chelsea, N'Golo Kante, zai yi jinyar mako uku sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa, a cewar kocin kungiyar Frank Lampard.

Dan wasan na Faransa wanda ya lashe Kofin Duniya ya yi raunin ne lokacin fafatawar da Manchester United ta doke su da ci 2-0 ranar Litinin.

Jinyar da zai yi babban koma-baya ne ga Chelsea, wacce za ta buga wasan lig shida da kuma cup games a mako ukun da ke tafe.

"Ya ji rauni a tsokarsa, irin wanda ya ji lokacin wasanmu," in ji Lampard.

Kante zai yi jinya ne a lokacin da Chelsea ke tsaka mai wuya a kakar wasa ta bana.

Chelsea za su fafata da Bayern Munich a wasan 'yan 16 na gasar Zakarun Turai ranar Talata mai zuwa sannan su sake karawa a Jamus ranar 10 ga watan Maris.

Chelsea, wacce ita ce ta hudu a saman teburin Firimiya amma bata ci wasa a karawarta a wasa hudu mafi muhimmanci ba, za ta gwabza da Tottenham a wasan hamayya da za su yi a London ranar Asabar.

Kazalika, za su karbi bakwancin Liverpool a zagaye na biyar na gasar cin Kofin FA ranar uku ga watan Maris, yayin da za su fuskanci Bournemouth da Everton a gasar Firimiya a ranar 29 ga watan Fabrairu da takwas ga watan Maris.