Hazard ya karya kafa ba zai buga wasan Man City ba

Real Madrid

Asalin hoton, Reuters

Eden Hazard ba zai buga wa Real Madrid wasan da za ta yi da Manchester City ba, sakamakon karya kafa da ya yi.

A ranar 26 ga watan Fabrairu Real Madrid za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan farko na zagaye na biyu a gasar Champions League.

Hazard, mai shekara 29, ya karya kafa ne a wasan da Levante ta doke Real Madrid 1-0 ranar Asabar a gasar La liga, inda Jose Luis Morales ya ci kwallon saura minti 11 a tashi daga wasa.

A makon jiya dan kwallon tawagar Belgium ya warke daga jinyar wata uku, sai kuma yanzu ya kara yin wani raunin kusan irin wanda ya ji a baya.

Yawan jinya da tsohon dan kwallon Chelsea ke yi a Real ya sa karawa 15 ya buga mata tun komawarsa Santiago Bernabeu a bara.

Wannan raunin da ya ji na nufin ba zai buga wasan hamayya na El Clasico ba kenan da Barcelona ranar 1 ga watan Maris.

A shekarar 2017, dan wasan ya fara karya kafarsa ta hagu a Chelsea, ciwo da ya kara ji a watan Nuwamba, sannan ya kara wani ranar Asabar.