Cristiano Ronaldo ya ci kwallo a wasansa na 1,000

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Asabar Juventus ta je ta ci SPAL 2-1 a wasan mako na 25 a gasar Serie A da suka fafata.

Juventus ta ci kwallayenta ta hannun Cristiano Ronaldo da kuma Ramsey, ya yin da Spal ta zare daya ta hannun Petagna.

Wasan da Ronaldo ya buga shi ne na 1,000 tun lokacin da ya zama kwararren dan kwallon kafa.

Haka kuma kwallon da Ronaldo ya ci a wasan ya zama ta 11 a jere yana leka gidan kifi kenan.

Nasarar da Juventus ta yi ya sa ta bayar da tazarar maki hudu, yayin da abokan hamayyarta Lazio da Inter Milan za su buga wasanninsu ranar Lahadi.

Jumulla Ronaldo dan wasan tawagar Portugal ya ci kwallo 16 a Serie A ta bana, bayan da ya ke zura kwallo a jere a karawa 11 kawo yanzu.

Haka kuma ya ci kwallo 36 a bana a Juventus da 36 da ya ci wa Portugal, ana kuma sa ran zai doke tarihin cin kwallaye a jere a gasar Serie A ranar 1 ga watan Maris lokacin da za su fafata da Inter Milan a wasan mako na 26.