Man United ta koma ta biyar a teburin Premier

Man United

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta yi nasarar doke Watford da ci 3-0 a wasan mako na 27 a gasar cin kofin Premier da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.

United ta fara cin kwallo ta hannun Bruno Fernandes a bugun fenariti daf da za a je hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, United ta kara kwallo ta hannun Anthony Martial, sannan Mason Greenwood ya kara na uku.

Da wannan sakamakon United ta hada maki 41 ta koma ta biyar a teburin Premier da tazarar maki uku tsakaninta da Chelsea ta hudu.

Saura minti 10 a tashi daga wasan dan kwallon tawagar Super Eagles Odion Ighalo ya canji Martial, sai dai bai ci kwallo ba.

A watan Janairu ne Ighalo ya koma United da buga wasannin aro daga China.

Ita kuwa Watford tana nan a matakinta nan 19 da makinta 24, bayan wasan mako 27 da ta yi a gasar bana.

United za ta ziyarci Everton a wasan mako na 28 a gasar Premier ranar 1 ga watan Maris, ya yin da Watford za ta karbi bakuncin Liverpool ranar 29 ga watan Fabrairu.