Yadda Baby da Ramsy suka dambata a Nasarawa

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon dambe tsakanin Baby da Ramsy

An dambata a wasanni da dama a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke Marabar Nyanya a jihar Nasarawa, ciki har da damben mata.

Baby da Ramsy sun bukaci yin dambe don kashin kansu, inda Baby ta wakilci jihar Nasarawa, ita kuwa Ramsy tana bangaren Kano.

Ko da yake turmi biyu suka yi babu kisa aka raba su.

Cikin wasannin da aka yi kisa:

  • Coronavirus daga Kudu ya buge Bahagon Gidewe
  • Shagon Wale ya yi nasara a kan Shagon Ali Kanin Bello
  • Karda bakon dole ya yi rashin nasara a hannun Bahagon Alin bata isarka
  • Shagon Tanko Guramada ya buge Dogon Inda daga Jamus
  • Garkuwan Cindo Guramada ya doke Bahagon Sisco daga Kudu

Damben da bai yi kisa ba:

  • Shagon Aljanin Arewa da Kato Mai karfi daga Kudu
  • Shagon Lawwali daga Arewa da Goloko daga Kudu
  • Coronavirus daga Kudu da Shagon Aljanin Arewa
  • Tula daga Jamus da Shagon Kunnari Suda daga Kudu
  • Dogon Na Sigari daga Kudu da Shagon Goshin jirgi daga Arewa