Jigawa ta ci Wikki Tourist a Firimiyar Najeriya

Nigerian Premier League

Asalin hoton, NPFL

Jigawa Golden Stars ta yi nasarar doke Wikki Tourist da ci 2-1 a wasan mako na 21 da suka kara ranar Lahadi a Kano.

Minti biyu da fara wasa ne Wikki ta fara cin kwallo ta hannun Promise Damala, kuma haka suka je hutu da kwallo daya a raga.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Jigawa ta farke ta hannun Ibrahim Saleh, sannan Abdullahi Lala ya kara na biyu.

Kano Pillars ma rashin nasara ta yi da ci 2-1 a gidan Rivers United.

Rivers ta fara cin kwallo ta hannun Konan Ruffin N'Gouan a bugun fenariti, sannan Cletus Emotan ya ci na biyu saura minti biyu a tashi wasa.

Kyaftin din Pillars, Rabiu Ali shi ne ya zare kwallo daya daf da alakalin wasa zai tashi karawar.

Ita kuwa Plateau United wadda take ta daya a teburi ta je ta tashi 0-0 a gidan Lobi wadda take ta biyu a teburin wasannin bana.

Sakamakon wasannin mako na 21 da aka yi:

  • Lobi Stars 0-0 Plateau United
  • Akwa United 1-1 Warri Wolves
  • Rivers United 2-1 Kano Pillars
  • MFM 0-0 Heartland
  • Adamawa United 2-1 FC Ifeanyiubah
  • Sunshine Stars 0-0 Rangers
  • Katsina United 1-0 Abia Warriors