Arsenal ta kara yin sama a teburin Premier.

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta doke Everton da ci 3-2 a gasar cin kofin Premier karawar mako na 27 da suka fafata ranar Lahadi a Emirates.

Eveton ce ta fara cin kwallo ta hannun Dominic Calvert-Lewin minti daya da fara wasa, sai dai kuma Gunners ta farke ta hannun Eddie Nketiah daga baya.

Arsenal ta kara na biyu ne ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang kuma haka suka je hutu.

Bayan da suka koma wasa ne Pierre-Emerick Aubameyang ya kara cin na biyu kuma kwallo na uku da Arsenal ta zura a raga.

Sai dai minti uku tsakani Richarlison de Andrade ya ci wa Everton kwallo na biyu da ta sa a ragar Gunners a Emirates.

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta tara a teburin Premier da maki 37, bayan buga karawa 27.

Ita kuwa Eveton tana ta 11 da maki 36 a teburin na wasannin bana.

Arsenal za ta ziyarci Manchester City ranar 1 ga watan Maris a wasan mako na 28, a kuma ranar Everton za ta yi wa Manchester United masauki.