Barcelona ta bayyana wadanda za su kara da Napoli

bARCELONA

Asalin hoton, Getty Images

Napoli ta karbi bakuncin Barcelona a wasan farko na zagaye na biyu a gasar Champions League da za su kara ranar Talata.

Barcelona ta kawo wannan zagayen, bayan da ta yi ta daya a rukuni na shida da maki 14, Napoli kuwa ta biyu ta yi a rukuni na biyar da maki 12.

Wannan ne karon farko da Napoli da Barcelona za su fafata a gasar Champions League a tsakaninsu.

Napoli ba ta taba daukar Champions League ba, ita kuwa Barcelona tana da shi guda biyar.

A karshen mako ne Barcelona ta doke Eibar a gasar La Liga da ci 5-0, ita kuwa Napoli nasara ta je ta yi da ci 2-1 a gidan Brescia a gasar Serie A.

'Yan wasa shida ne daga karamar Barca ta je da su Italiya don buga wasan Champions League din.

Kawo yanzu Luis Suarez da Ousmane Dembele da Jordi Alba da kuma Sergi Roberto na jinya.

Haka kuma kungiyar ta Camp Nou ta je Italiya da dan wasan Denmark da ta dauka da gaggawa wato Martin Braithwaite sai dai buga karawar ba, sakamakon ba a yi masa rijista ba

'Yan wasan Barcelona da aka je da su Napoli

Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Sergio Busquets da Arthur da Messi da Neto da Lenglet da Griezmann da kuma Braithwaite.

Sauran sun hada da De Jong da Vidal da Umtiti da Junior da Inaki Pena da Riqui Puig da Alex Collado da Ansu Fati da Ronald Araujo da kuma Sergio Akieme.