Effiong ne kan gaba a cin kwallo a Firimiyar Najeriya

Nigerian Premier League

Asalin hoton, NPFL

Dan wasan Akwa United, Ndifreke Effiong shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Firimiya Najeriya.

A karshen mako na aka yi fafatawar sati na 21, kuma kawo yanzu Effiong yana da 10 a raga.

Victor Mbaoma na Enyimba International ya ci guda tara, shi ne na biyu a jere wadan da ke kan gaba a cin kwallo a gasar.

'Yan wasa uku ne ke kan-kan-kan da suka zura takwas a raga kowannensu da ya hada da Tasi'u Lawan na Katsina United.

Sauran sun hada da Ibrahin Mustapha Plateau United da Israel Abia na Rangers International.

Bayan buga wasannin mako na 21, Plateau United tana a mataki na daya da maki 37.

Rivers United ta biyu da maki 36, sai Lobi Stars ta uku wadda ita ma makinta 36.

Sakamakon wasannin mako na 21:

 • Jigawa Golden Stars 2-1 Wikki Tourists
 • Lobi Stars 0-0 Plateau United
 • Akwa United 1-1 Warri Wolves
 • Rivers United 2-1 Kano Pillars
 • MFM 0-0 Heartland
 • Adamawa United 2-1 FC Ifeanyiubah
 • Sunshine Stars 0-0 Rangers
 • Katsina United 1-0 Abia Warriors
 • Nasarawa United 2-0 Enyimba

Wasannin mako na 22 da za a buga ranar 1 ga watan Maris

 • Kwara United da Lobi Stars
 • Plateau United da Jigawa Golden Stars
 • Heartland da Rivers United
 • Kano Pillars da Dakkada
 • Rangers da Adamawa United
 • FC Ifeanyi Ubah da MFM
 • Abia Warriors da Akwa United
 • Warri Wolves da Sunshine Stars
 • Wikki Tourist da Nasarawa United