An fitar da jadawalin kwallon Afirka na CHAN 2020

CHAN 2020

Asalin hoton, Getty Images

Mai masaukin baki, Kamaru, za ta fafata da Zimbabwe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke taka-leda a gida wato CHAN.

Tawagar kwallon kafa ta Kamaru da ta Zimbabwe za suyi bikin bude gasar shekarar nan ranar 4 ga watan Afirilu.

Indomitable Lions za ta fafata da Zimbabwe a filin wasa na Ahmadou Ahidjo, wanda a nan ne za a buga karawar karshe ranar 25 ga watan Afirilu.

Mai rike da kofin Morocco za ta fara karawa da Togo ranar 6 ga watan Afirilu, kafin ta fafata da Rwanda da kuma Uganda a rukuni na uku.

Buga gasar ta CHAN da za a yi da ta kunshi 'yan wasa da ke taka-leda a gida ta sa an sauya lokacion karkare gasar zakarun Afirka ta Champions League da ta Confederation Cup zuwa wata biyu.

Domin ganin cikakken jadawalin CHAN 2020 Latsa nan