Za a tursasa wa Arsenal ta sayar da Aubameyang, Xhaka 'ba zai sake wasa a Arsenal ba'

Arsenal striker Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, NEIL HALL

Za a iya tursasa wa Arsenal ta sayar da dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang idan suka gaza sasantawa kan sabon kwantaragi yayin da kwantaragin dan wasan mai shekara 30 zai kare a 2021. (Star)

Tsohon kocin Everton Sam Allardyce ya ce ya yi yunkurin sayo Aubameyang daga Borussia Dortmund kafin dan wasan ya koma Arsenal. (Talksport)

Dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 19, zai iya ci gaba da zama a Dortmund fiye da kakar wasa ta bana duk da rade radin da ake yi cewa a bazara zai koma Chelsea,Liverpool ko Manchester United. (Ruhr Nachrichten - in German)

Dan wasan RB Leipzig dan kasar Jamus Timo Werner, mai shekara 23, wanda ake hasashen zai koma Liverpool, zai samu kudin fita euro 30m da kuma karin alawus-alawus, ba kamar yadda a baya aka ce za a ba shi £50m ba. (Sport1 - in German)

Leicester City na shirin sabunta kwantaragin Christian Fuchs, mai shekara 33, a yayin da kwantaragin dan kasar ta Austria ke shirin karewa. (Mail)

Ana sa ran dan wasan Manchester United Nemanja Matic, mai shekara 31, zai bar kungiyar idan kwantaraginsa ya kare a bazara, a yayin da jam'insa ke duba zabin da ke gaban dan wasan, sai dai AC Milan ta ce ba ta sha'awar sayensa saboda kudin da aka tsuga a kan dan kasar ta Serbia. (Calciomercato)

Dan wasan Arsenal Granit Xhaka, mai shekara 27, ya ce yana jin tsoron cewa ba zai sake buga wa kungiyar tamaula ba bayan ihun da ya yi wa magoya bayan kungiyar lamarin da ya sa aka tube shi daga mukamin kyaftin - kuma yana tantama kan ko zai sake karbar kyaftin din(Evening Standard)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Roma da Manchester United na ci gaba da tattaunawa kan mayar da zaman aron da Chris Smalling, mai shekara 30 yake yi ya koma na din-din-din (Star)

Smalling ya ce "zai yanke shawara ta ban mamaki" - ko ya ci gaba da zama a Manchester United ko kuma ya koma Roma din-din-din.(Sky Sports)

Everton na son sayen dan wasan bayan Lille dan kasar Brazil Gabriel, mai shekara 22, a yayin da suke so su karfafa tsakiyarsu kafin lokacin musayar 'yan kwallo a bazara. (Mirror)

Har yanzu shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge bai gamsu da wasan dan kasar Brazil Philippe Coutinho ba. Kungiyar ta Jamus na da zabin sayar wa Barcelona dan wasan mai shekara 27 wanda yake can a matsayin aro. (Bild, via Mail)

Mahaifin dan wasan Chelsea dan kasar Spain Marcos Alonso, mai shekara 29, ya ce mai yiwuwa dan nasa zai koma Italiya, bayan da ya buga wasa Fiorentina kafin ya koma Stamford Bridge. (Calciomercato - in Italian)

Dan kasar Morocco Hakim Ziyech, mai shekara 26, ya ce kocin Chelsea Frank Lampard ya taka muhimmiyar rawa a matakin da ya dauka na komawa Chelsea daga Ajax. (Mail)

Leeds suna son sayo 'yan wasa hudu a bazara a kan £45m a yayin da suka samu tagomashi a gasar cin Kofin Firimiya. (Express)