Mai kuke son sani kan wasan Real da Man City?

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan farko zagaye na biyu a gasar Champions League da za su kara ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Real ce ta yi ta biyu a rukunin farko da maki 11, ita kuwa Manchester City ce ta daya a rukuni na uku da maki 14.

Wannan ne wasa na biyar da kungiyoyin za su kara a gasar ta Zakarun Turai, inda Real ta ci wasa biyu da canjaras biyu.

Haka kuma kungiyar ta Santiago Bernabeu ta ci kwallo biyar ita kuwa Manchester City ta zura uku a raga.

Real Madrid ta lashe Champions League sau 13, ya yin da har yanzu City ba ta taba daukar kofin ba.

A karshen mako ne Leavante ta ci Real Madrid 1-0 a gasar La Liga, ita kuwa City zuwa ta yi ta doke Leicester City 1-0 a gasar Premier.

Kawo yanzu Manchester City ba ta da wani dan kwallo da ke jinya, ita kuwa Real tana da masu rauni biyu wato Asensio da kuma Eden Hazard.

Za su fafata a wasa na biyu a gasar ta Champions League a Etihad ranar 17 ga watan Maris.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Militao da Ramos da Varane da Marcelo da kuma Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.

Masu cin kwallo: Benzema da Bale da Lucas Vazquez da Jovic da kuma Vinicius Jr.

'Yan wasan Manchester City:

Masu tsaron raga: Ederson da kuma Scott Carson

Masu tsaron baya: Kyle Walker da John Stones da Oleksandr Zinchenko da Aymeric Laporte da Benjamin Mendy da Joao Cancelo da Nicolas Otamendi da kuma Eric Garcia.

Masu buga tsakiya: Raheem Sterling da Ilkay Gundogan da Kevin De Bruyne da Rodrigo da Bernardo Silva da David Silva da Fernandinho da kuma Phil Foden.

Masu buga gaba: Sergio Aguero da Gabriel Jesus da kuma Riyad Mahrez

Wadanda za su yi alkalanci wasan:

Alkalin wasa

  • Daniele Orsato daga Italiya

Mataimakan alkalin wasa

  • Lorenzo Manganelli daga Italiya
  • Alessandro Giallatini daga Italiya

Mai jiran kar-ta-kwana

  • Daniele Doveri daga Italiya

Mai kula da VAR

  • Massimiliano Irrati daga Italiya

Mataimakin mai kula da VAR

  • Ciro Carbone daga Italiya