Kudin shiga ya ragu a Manchester United

Man United

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta yi rashin kudin shiga zuwa kaso 12 cikin 100 a wata Shida zuwa Disamba, saboda ba ta buga Champions League.

Kudin nuna wasannin United a talabijin ya yi kasa zuwa kaso 33.4 ciki 100, koda yake ta samu karin kudin tallace-tallace da ya kai kaso 6.5 cikin 100.

Sai dai kuma kudin shiga kallon wasannin Manchester United na nan yadda yake.

United na sa ran samun kudin shiga a shekarar 2020 tsakanin fam miliyan 560 zuwa 580.

Mataimakin shugaban United, Ed Woodward ya ce sun yi nasarar bunkasa 'yan kwallo ta waje sayo sabbin 'yan wasa.

Ya kara da cewar 'yan wasan da United ta saya da wadanda ta dauko daga karamar kungiyar ya fayyace ginin da suke na bunkasa tafiyar da za a ci riba nan gaba.

Edwood ya ce yana fatan United za ta kare a gurbi mai kyau a Premier ko lashe Europa da kuma FA Cup a bana.

A shekarar 2019 United ta sanar da samun kudi da ya kai fam miliyan 627 - hakan ya sa kungiyar ta koma ta uku a jere wadanda suka samu kudin shiga mai tsoka a duniya a fannin tamaula.

Wani kamfanin kididdigar samun kudi da kashewa da hada-hada a kwallon kafa wato Deloitte ne ya fayyace wadanda ke kan gaba a samun kudi a fannin kwallon kafa.

Barcelona ce ke kan gaba a 2019, sai kuma Real Madrid ta biyu, sannan United ta uku.