Bayern Munich ta saka Chelsea cikin matsi

Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta yi rashin nasara da ci 3-0 a hannun Bayern Munich a wasan farko zagaye na biyu a Champions League da suka kara a Stamford Bridge.

Serge Gnabry ne ya fara cin kwallo, sannan minti uku tsakani ya kara na biyu daga baya Robert Lewandowski ya kara na uku.

Bayern wadda ke ta daya a gasar Bundesliga ta bi sahun RB Leipzig wadda ta yi nasarar cin Tottenham 1-0 a makon jiya a Ingila.

Tun farko kungiyoyin biyu sun kammala minti 45 babu ci sannan suka je hutu.

Bayan da suka koma zagaye naq biyu ne Munich ta ci kwallayen gabaki daya da hakan zai kara mata kwarin gwiwa idan an je gidanta.

Haka kuma Chelsea ta karasa fafatawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Marcos Alonso jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Lewandowski.

Shi kuwa Jorgingo dan wasan Chelsea da ta saya da tsada ba zai buga karawa ta biyu ba, bayan da aka yi masa katin gargadi guda biyu.

Chelsea ba ta taba yin rashin nasara a gasar Champions League da kungiyar Jamus a Stamford Bridge ba, sai wannan karon.

Kuma wasa na biyar kenan da Chelsea da Bayern ke haduwa a gasar zakarun Turai kuma ta hudu a Champions League.

Kawo yanzu Bayern ta ci fafatawa biyu kenan, ita Chelsea ta yi nasara a daya da canjaras biyu.

Bayern Munich za ta karbi bakuncin Chelsea a wasa na biyu ranar 18 ga watan Maris a Jamus.

Asalin hoton, BBC Sport