Napoli da Barcelona sun tashi kunnen doki 1-1

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta je ta tashi kunnen doki 1-1 da Napoli a wasan farko na zagaye na biyu a gasar Champions League da suka kara ranar Talata.

Dries Mertens ne ya fara cin Barcelona kwallo, hakan kuma ya sa ya yi kan-kan-kan da Marek Hamsik da ya ci wa Napoli kwallo 121 a tarihi.

Sai dai bayan da aka koma zagaye na biyu ne Barcelona ta farke ta hannun Antoine Griezmann, daga kwallon da Nelson Semedo ya buga masa.

Barcelona ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Arturo Vidal jan kati.

Saura minti daya a tashi wasa ne Vidal ya yi wa Fabian Ruiz keta, sai Ruiz ya kalubalance shi, nan da nan dan wasan Barca ya sa hannu a fuskar dan kwallon Napoli ya kuma ture shi.

Dalilin da ya sa alkalin wasa ya daga wa Vidal katin gargadi biyu a lokaci daya.

Barcelona za ta karbi bakuncin karawa ta biyu ranar 18 ga watan Maris, sai dai shima Sergio Busquets ba zai buga karawar ba.

Asalin hoton, BBC Sport