Manchester Utd ta kara azama don dauko Grealish, Juve sun so sayo Guardiola

Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United sun kara azama a yunkurinsu na sayen dan wasan Aston Villa mai shekara 24 Jack Grealish. (Manchester Evening News)

Mai yiwuwa United ta sayar da dan wasan Ingila Jesse Lingard, mai 27, da takwaransa dan kasar Brazil Andreas Pereira, mai shekara 24, a karshen kakar da muke ciki (Express)

Arsenal za su iya amincewa da tayin da aka yi musu kan Pierre-Emerick Aubameyang a kakar wasan da muke ciki domin guje wa rasa dan wasan mai shekara 30 ba tare da samun ko kwabo ba lokacin musayar 'yan kwallo.(Mail)

Wani zabin kuma shi ne, har yanzu Aubameyang bai kawar da yiwuwar sanya hannu a kan sabon kwantaragi a Arsenal ba ko da yake tattaunawa a kan hakan ta cije. (Metro)

Shugaban Juventus Andrea Agnelli ya ce kungiyarsa ta duba yiwuwar tunkarar kocin Manchester City Pep Guardiola da zummar dauko shi. (Manchester Evening News)

Inter Milan ta ce Aubameyang ne dan wasa na farko da take son saya lokacin musayar 'yan kwallo idan dai dan wasan Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, ya bar kungiyar a bazara. (Calciomercato)

Real Madrid na sanya ido kan dan wasan Crystal Palace dan kasar Norway Alexander Sorloth, mai shekara 24, wanda ya zura kwallo 21 a wasa 30 da ya buga lokacin da Trabzonspor ta yi aronsa a kakar wasa ta bana. (Evening Standard)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kudin da aka tsuga kan dan wasan Liverpool Philippe Coutinho na nufin Barcelona za ta biya Liverpool din £225m domin sayo dan wasan Senegal Sadio Mane, mai shekara 27 (Mirror)

Manyan 'yan wasan Manchester City ka iya barin kungiyar, cikinsu har da dan wasan Ingila mai shekara 25, Raheem Sterling, idan suka lashe gasar Zakarun Turai a kakar wasa ta bana. (ESPN)

Arsenal na sha'awar sayen dan wasan Spain da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 21, Marc Cucurella, kuma a shirye suke su biya £20m domin sayo dan wasan, wanda a yanzu haka Getafe ta yi aronsadagaBarcelona.(Cadena Cope via Sport Witness)

Dan wasanReal Madriddan kasar Spain Sergio Ramos, mai shekara 33, bai nuna zakuwar sanya hannu kan sabon kwantaragi da Bernabeu amma ya ce dangantakarsa da kungiyar "tana da gwabi". (Goal)

Kocin Spain Luis Enrique ya damu da rashin azamar golanChelsea Kepa Arrizabalaga mai shekara 25 a baya bayan nan a yayin da suke shirin fara gasar Turai ta bazara. (AS - in Spanish)

Tsohon Arsenal Arsene Wenger ya ce ya fahimci cewa dan wasan Bayern Munich mai shekara 24 dan kasar Jamus Serge Gnabry zai ci gaba da zama a Arsenal. (beIN Sports, via Metro)