Man City ta daukaka kara zuwa kotun wasanni

Etihad Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester City ta daukaka kara a kotun sauraren kararrakin wasannin ta duniya wato Cas.

City ta yi hakan ne bayan da hukumar kwallon kafar Turai, UEFA ta dakatar da kungiyar ta Etihad daga shiga wasannin Champions League kaka biyu.

Haka kuma UEFA ta ci tarar City fam miliyan 25, saboda samunta da laifin karya ka'idar cinikayyar da kungiya ya kamata ta yi a kakar tamaula.

Babban jami'i a City, Ferran Soriano ya ce ''Zargin karya ka'idar hukumar ta UEFA ba gaskiya bane''.

Manchester City wadda ba ta taba lashe Champions League ba, za ta fafata da Real Madrid mai 13 a wasan zagaye na biyu ranar Laraba.

City tana mataki na biyu a teburin Premier da tazarar maki 22 tsakaninta da Liverpool wadda take jan ragamar wasannin shekarar nan.

Labarai masu alaka