Lewandowski ba zai buga karawa da Chelsea ba

Bayern Munich Hakkin mallakar hoto Getty Images

Robert Lewandowski ba zai buga wasa na biyu da Bayern Munich za ta karbi bakuncin Chelsea a gasar Champions League ba.

Lewandowski ya ji rauni ne a Stamford Bridge, an kuma ce zai yi jinyar mako hudu kan ya koma taka leda.

Dan wasan tawagar Poland shi ne ya bayar da kwallo biyun da Serge Gnabry ya ci, sannan da kansa ya kara na uku a karawar da suka doke Chelsea 3-0 ranar Talata a Stamford Bridge.

Bayern Munich ta ce Lewandowski ya ji raunin ne a wasa da Chelsea a ketar da Marcos Alonso ya yi masa.

Watakila dan kwallon mai shekara 31, ba zai yi wa Bayern wasa shida ba.

Lewandowski ya ci kwallo 39 a wasa 33 da ya buga wa Bayern Munich a bana.

Bayern wadda take ta daya a teburin Bundesliga za ta buga wasa hudu a Lik da German Cup da za ta buga daf da na kusa da na karshe da Schalke.

Daga nan ne za ta karbi bakuncin Chelsea a wasa na biyu a Champions League ranar 18 ga watan Maris.

Labarai masu alaka