Babayaro ya kalubalanci aikin kocin Yobo

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon dan wasan Chelsea, Celestine Babayaro ya ce ya yi murna da ake saka tsoffin 'yan wasan Najeriya aikin kocin kasar.

Sai dai Babayaro ya kalubalanci shaidar takardun aikin kocin Joseph Yobo.

Tsohon dan wasan Super Eagles ya yi wannan kalaman, bayan da aka bai wa Yobo aikin mataimakin kocin tawagar kwallon kafar Najeriya.

Babayaro, wanda ya lashe zinare a gasar Olympic a Atlanta a 1996 ya ce duk wani aiki da za a bai wa mutum ya kamata yana da takardar shaidar kwarewa a kai.

Babayaro da Yobo sun buga wa Super Eagles gasar kofin duniya a 2002 da kuma ta nahiyar Afirka shekara biyu tsakani da aka yi a Tunisia.

Babayaro ya ce ''Ban damu ba ko tsohon dan wasa ne koma wanene, amma a tabbatar an bai wa wanda ya dace''.

''Bana jin yana da shaidar aikin koci, amma a dunga tabbatar da shaidar aiki kan a nada mutum.

''Yobo ya yi kyaftin a Super Eagles ya kuma taka rawar gani, amma idan ka shirya nada shi kan wannan matakin, ka tabbatar yana da kwarewa.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan akin mataimakin kocin Najeriya da aka bai wa Yobo.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta ce bai wa Joseph Yobo aiki zai sa a samu kyakkyawan jagoranci, sannan 'yan kwallo za su yi koyi da bajintar da ya yi a baya.

Labarai masu alaka