An tuhumi Dele Alli da kalamai kan coronavirus

Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty Images

An tuhumi dan wasan Tottenham, Dele Alli kan kalaman da ya yi na coronavirus a shafin sada zumunta.

Alli, mai shekara 23, ya saka wani bidiyo a shafinsa na sada zumunta a Snapchat, inda yake barkwanci kan barkewar coronavirus.

A bidiyon an fahimci yana yi wa wani mutun dan nahiyar Asiya shakiyanci ne.

Daga baya ya cire bidiyon, sannan ya sake yin wani ya kuma nemi gafara da cewar bai kyauta ba, ya kuma zubar da kimarsa da ta kungiyarsa.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi dan wasan da halin rashin kyautawa da karya doka kai tsaye.

An bai wa dan kwallon nan da ranar Alhamis 5 ga watan Maris domin ya kare kansa.

Labarai masu alaka