An samu Zakaru a wasannin makarantun sakandare a Abuja

School Sport Hakkin mallakar hoto Maltina School Sport

A ranar Alhamis aka karkare wasan tsalle-tsalle da guje-guje na makarantun sakadaren Najeriya a babban birnin tarayya, Abuja.

Kimanin maza 44 da kuma mata 44 ne suka samu gurbin shiga wasan karshe da za a yi nan gaba a jihar Legas.

Gasar wadda take ta matasa tun daga shekara 14 zuwa 18, ta kunshi kanana da manyan makarantun sakandaren Najeriya.

Wannan ne karon farko da aka fara gasar mai dauke da wasan tseren mita 100 da na 800 da na 100 na yan wasa hudu da tsallen shinge da na badake da na jifan mashi da kuma na jifan dalma.

An shirya wasannnin ne don zakulo matasan 'yan wasa da za su dunga wakiltar Najeriya nan gaba a wasanni da dama.

A ranar 28 ga watan Fabrairu za a karkare a gasar da jihar Kano ke karbar bakuncin wasannin da ake yi a jami'ar Ado Bayero.

Hakkin mallakar hoto Maltina School Sport

Daga nan za a fitar da wadanda suka yi nasara, domin su je jihar Legas donm buga wasan karshe.

Duk makarantar da ta yi nasara za ta lashe naira miliyan biyar da ake sa za ta yi amfani da kudin don bunkasa wasanninta.

Jihar Legas ce za ta karbi bakuncin wasannin karshe ranar 9 ga watan Maris a kwalejin kimiya da fasaha da ke Yaba.

Labarai masu alaka