An yi wa Anceloti jan kati a karawa da United

Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Eveton da Manchester United sun tashi wasa 1-1 a gasar Premier karawar mako na 28 da suka yi a Goodison Park ranar Lahadi.

Minti uku da fara wasa mai masukin baki, Everton ta ci kwallo ta hannun Dominic Calvert-Lewin, kuma na 15 da ya ci a wasannin bana.

An ci United ne, bayan da mai tsaron raga David de Gea ya yi kokarin buge kwallo, amma sai ta je wajen Dominic Calvert-Lewin kai tsaye.

United ma ta farke kwallo ne, bayan da mai tsaron ragar Everton, ya kasa tare kwallon da Bruno Fernandes ya buga masa ta fada raga.

Tun farko Nemanja Matic ne ya buga kwallo ta bugi turke a minti na 31 ne Manchester United ta zare kwallon da aka ci ta wasan ya koma 1-1.

Everton ta kasa kwantar da hankali a wasan, inda aka bai wa 'yan wasanta bakwai katin gargadi.

Haka kuma mai masukin baki ta kusan zura kwallo a raga, bayan da Gylfi Sigurdsson ya yi bugun tazara, amma kwallon ya bugi turke.

Daga baya masu tsaron ragar kungiyoyin biyu sun taka rawar gani, inda suka hana kwallaye shiga ragarsu.

Daf da za a tashi wasa ne Calvert-Lewin ya ci kwallo, amma na'urar VAR ta ce ba ta ci ba, an yi satar gida.

Hakan ya biyo bayan da Sigurdsson na zaune shi kadai a gaban De Gea duk da bai taba kwallon ba ta fada raga aka ce satar gida ya yi.

Dalilin da ya sa Ancelotti ya kalubalanci alkalin wasa, wanda ya daga masa jan kati kai tsaye, bayan da ya tashi karawar.

Da wannan sakamakon United ta yi wasa takwas ba a doke ta ba kenan, tana nan a matakinta na biyar a teburin Premier.

Ita kuwa Everton ta ci karo da tsaiko na fatan da take na shiga gurbin Europa League na badi, bayan da Wolves ta ci Tottenham 3-2 ranar Lahadi.