Plateau ta ci Jigawa tana nan ta daya a teburi

Nigerian Premier League

Asalin hoton, Npfl

Plateau United ta yi nasara doke Jigawa Golden Stars da ci 2-1 a wasan mako na 22 a gasar Firimiyar Najeriya da suka fafata ranar Lahadi.

Tun kan hutu ne Plateau ta ci kwallo ta hannun Salefu Oche Ochowechi, sannan Tosin Omoyele ya ci na biyu saura minti takwas su je hutu.

Daf da za a tashi daga wasanne Jigawa ta zare kwallo daya ta hannun Saleh Ibrahim.

Da wannan sakamakon Plateau tana nan ta daya a kan teburi da maki 40 da tazarar maki daya tsakaninta da Rivers mai maki 39, ita ma Lobi Stars maki 39 ne da ita.

Jigawa Golden Stars kuwa tana ta 19 da maki 23 da tazarar maki uku tsakaninta da Adamawa United ta karshen teburi wato ta 20.

Sakamakon wasannin mako na 22 da aka yi:

  • Kwara United 0-1 Lobi Stars
  • Kano Pillars 2-0 Dakkada
  • Heartland 0-2 Rivers United
  • FC Ifeanyiubah 1-0 MFM
  • Rangers 2-0 Adamawa United
  • Wolves 3-0 Sunshine Stars
  • Abia Warriors 2-1 Akwa United
  • Wikki 1-0 Nasarawa Utd