Shin ka taba ganin amarya a damben gargajiya kuwa?

Shin ka taba ganin amarya a damben gargajiya kuwa?

Wannan ita ce amaryar dambe da aka yi tsakanin Boloko daga Kudu da Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Jamus.

Koda yake turmi daya kawai suka yi aka raba su ba tare da wani ya je kasa ba.

Kuma daya ne daga cikin damben da aka a gidan wasa na Idris Umar Bambarewa da ke Marabar Nyanya jihar Nasarawa ranar Lahadi.

Wasannin da aka yi kisa:

  • 'Yar tsalar Shamsu ya buge Shagon Boloko
  • Shagon Jimama ya kashe Lolu Shagon Dan Aminu
  • Shamsu Kanin Emi ya doke Kato Mai Karfi
  • Mustaphan Dan Shago ya kashe Shagon Shariff.

Damben da bai yi kisa ba:

  • Shagon Dogon Inda da Shagon Kunnari
  • Shagon Nasigari da Shagon Garkuwan Musa
  • Autan Mamman da Shagon Aleka
  • Boloko da Shagon Lawwalin Gusau