Man City ta lashe Carabao Cup na uku a jere

Caraboa Cup

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta yi nasarar kara lashe Carabao Cup, bayan da ta doke Aston Villa 2-1 ranar Lahadi a Wembley.

Manchester City ta fara cin kwallo a minti na 20 da fara wasa ta hannun Sergio Aguero, Haka kuma ta ci na biyu minti 10 tsakani ta hannun Rodri.

Saura minti hudu su je hutu ne Aston Villa ta zare daya ta hannun dan kwallon tawagar Tanzania, Mbwana Samatta.

A bara ne kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta lashe kofi uku da ya hada da Caraboa da Premier League da kuma FA Cup.

Manchester City ce ta lashe Caraboa na kakar 2017/18 da na 2018/19 da kuma na bana, kuma na bakwai da ta ci Jumulla.

Liverpool ce kan gaba a yawan lashe Caraboa a tarihi mai guda takwas, Manchester United biyar ne da ita iri daya da na Chelsea, Arsenal kuwa guda biyu take da shi.

Manchester City tana ta biyu a kan teburin Premier da maki 57 da kwantan wasa da Arsenal.

Ita kuwa Villa tana ta kasan teburi ta 19 da maki 25, bayan da ta buga karawar mako na 27 a gasar Premier shekarar nan.

A ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu, City ta je ta doke Real Madrid da ci 2-1 a gasar Champions League a Spaniya.

Sai a ranar 17 ga watan Maris Manchester City za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu a Etihad.

City wadda ke rike da FA Cup za ta ziyarci Sheffield Wednesdayranar 4 ga watan Maris a gasar FA Cup ta bana.

Asalin hoton, BBC Sport