Yadda Real Madrid ta doke Barcelona ta koma ta daya a teburi

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta yi nasarar cin Barcelona 2-0 a wasan mako na 26 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Real ta ci kwallon ta hannun Vinicius Junior saura minti tara a tashi daga wasan na hamayya da ake kira El Clasico.

Daf da za a tashi ne Real ta saka Mariano Diaz, kuma yana shiga fili ya ci Barcelona kwallo na biyu.

Da wannan sakamakon Real ta dare mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 56, ita kuwa Barcelona ta koma ta biyu da maki 55.

A wasan farko a gasar La Liga ta bana da suka hadu a Camp Nou ranar 18 ga watan Disamba tashi suka yi 0-0.

Rabon da Real ta ci Barcelona 2-0 a Santiago Bernabeu tun 16 ga watan Agustan 2017 a Spanish Super Cup.

Kafin Madrid ta kara da Barcelona ta yi rashin nasara a gidan Levante da ci 1-0 a gasar La Liga, sannan Manchester City ta doke ta 2-1 a Santiago Bernabeu.

Ranar 8 ga watan Maris Real Madrid za ta fafata da Real Betis a gasar La Liga, sannan ta ziyarci Manchester City a wasa na biyu na Champions League. ranar 10 ga watan nan.

Barcelona za ta karbi bakuncin Real Sociedad a gasar La Liga ranar 7 ga watan Maris, sannan ta karbi bakuncin Napoli a gasar Champions League ranar 10 ga watan Maris din.

Barcelona da Napoli sun tashi karawa 1-1 a wasan farko zagaye na biyu da suka fafata a Italiya ranar 25 ga watan Fabrairu.