Ancelotti zai san makomarsa bayan jan kati

Carlo Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Carlo Ancelotti zai san hukuncin da aka yanke masa, bayan jan kati da aka yi masa a karawar Everton da Manchester United ranar Lahadi.

Hukumar kwallon kafar Ingila za ta yi bitar rahoton alkalin wasa, daga nan ta dauki matakin ko dai na jan kunne ko cin tara ko kuma dakatarwa.

Dan kasar Italiya ya kalubalanci alkalin wasa, Chris Kavanagh, bayan da aka tashi daga wasa, bayan da aka soke kwallon da Dominic Calvert-Lewin ya ci aka ce akwai satar gida.

Idan aka yanke masa hukuncin dakatarwa, Ancelotti ba zai buga wasan da Everton za ta yi da tsohuwar kungiyarsa Chelsea.

Kocin mai shekara 60 ya ce bayan da aka tashi karawar 1-1 a Goodison Park, bai kaskantar da Kavanagh ba, wanda tun farko ya yi niyyar kwallo na biyu da Eveton ta ci daf da za a tashi.

Sai dai kuma na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci VAR ce ta ce akwai satar gida, bayan da Gylfi Sigurdsson na gaban mai tsaron ragar United, David de Gea.

Ancelotti ya kara da cewar ya yi magana da alkalin wasa a nutse ba tare da hayaniya ba.

Kocin na Everton shi ne na farko da aka bai wa jan kati, kuma hukuncin da aka kirkira a kakar bana.

Kungiyar masu taka leda ta duniya ce ta kirkiro hakan domin a samu da'a a wajen masu horas da tamaula a lokacin da ake wasanni.

Sai dai a bara hukumar kwallon kafa ta Ingila ta yi gwajin hukuncin.