Karim Benzema ya buga wa Real Madrid wasa 500

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid

A ranar Lahadi Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2-0 a wasan mako na 26 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata a Santiago Bernabeu.

Karim Benzema ya buga wa Real Madrid wasan na hamayya da ake kira El Clasico, kuma shi ne na 500 da ya buga wa kungiyar a dukkan fafatawa da ya yi mata.

Dan kasar Faransa ya fuskanci Barcelona kungiyar da ya fi yawan haduwa da ita da Atletico sau 34.

Kawo yanzu Benzema ya ci kwallo 240 a Real Madrid, kuma shi ne na shida a jerin wadan da suka ci wa kungiyar kwallaye da yawa a tarihi.

Wadanda suke kan gaba a ci wa Real kwallaye sun hada da na daya Cristiano Ronaldo mai 451, sai Raul na biyu da 323.

Di Stefano shi ne na uku mai kwallo 308, sannan Santillana shi ne na biyar wanda ya ci wa Real kwallo 242.

Ya fara buga wa Madrid wasa ranar 29 ga watan Agustan 2009 a kuma ranar farkon ya ci Deportivo La Coruna.

Kwana biyu tsakani ya kara cin kwallo a Santiago Bernabeu a karawa da Xerez.

Cikin wasa 500 da ya yi wa Real Madrid, Benzema ya buga gasar La Liga sau 337 da guda 100 a Champions League da 43 a Copa del Rey.

Ya kuma yi wasa 8 a kofin Zakarun nahiyoyin duniya da 8 a Spanish Super Cup da guda hudu a European Super Cup.

Dan wasan ya lashe kofin Champions League hudu da guda hudu na Zakarun nahiyoyin duniya da UEFA Super Cup uku da La Liga biyu da Copa del Rey biyu da Spanish Super Cup uku, jumulla yana da 18.