An dage wasan Juventus da Milan na Italian Cup

Italian Cup

Asalin hoton, Getty Images

Mahukuntan kwallon kafar Italiya, sun dage wasa na biyu na daf da karshe tsakanin Juventus da AC Milan a gasar Italian Cup.

Tun farko an tsara cewar kungiyoyin biyu za su fatata a karo na biyu karawar daf da karshe a filin wasa na Allianz ranar Laraba.

A wasan farko da suka kara ranar 13 ga watan Fabrairu a San Siro, Milan da Juventus sun tashi 1-1.

Ante Rebic ne ya fara ci wa Milan kwallo, Juventus ta farke a bugun fenariti daf da za a tashi ta hannun Cristiano Ronaldo.

Juventus ta doke Milan 1-0 ranar 10 ga watan Nuwambar 2019 a wasan gasar Serie A ta bana.

Juventus tana mataki na biyu a kan teburin Serie A da maki 60 da tazarar maki biyu tsakaninta da Lazio ta daya a teburin.

Ita kuwa Milan tana mataki na hudu da maki 54, bayan buga wasa na 24 a gasar Serie A.

Shima wasan da Napoli za ta karbi bakuncin Inter Milan a karawa ta biyu na Italian Cup din an soke shi.

A ranar 12 ga watan Fabrairu Napoli ta je ta doke Inter Milan 1-0 a San Siro.

Juventus ce kan gaba wajen lashe Italian Cup da 13 a tarihi, ita kuwa Milan guda biyar take da shi kawo yanzu.