Ingila za ta fafata da Belgium a Nations League

Tawagar kwallon kafa ta Ingila za ta fafata da ta Belgium a ajin farko a rukunin na biyu a UEFA Nations League a kakar 2020/21.

Ita kuwa Denmark za ta kece raini da Iceland a dai ajin farko a kungiyoyin da ke rukuni na biyun.

Wales za ta fuskanci Jamhuriyar Ireland da karawa tsakanin Finland da Bulgaria 'yan aji na biyu a rukuni na hudu.

Ita kuwa Ireland ta Arewa tana aji na biyu a rukunin farko da ya kunshi Austria da Norway da kuma Romania.

Za a fara wasannin farko a cikin watan Satumbar shekarar nan.

Yadda aka raba jadawalin:

Wasannin farko: 3-5 Satumba 2020

Wasanni na biyu: 6-8 Satumba 2020

Wasanni na uku: 8-10 Oktoba 2020

Wasanni na hudu: 11-13 Oktoba 2020

Wasanni na biyar: 12-14 Nuwamba 2020

Wasanni na shida: 15-17 Nuwamba 2020