Chelsea ta fitar da Liverpool daga FA Cup

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Chelsea ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a FA Cup, bayan da ta doke Liverpool da ci 2-0 ranar Talata a Stamford Bridge.

Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Willian Borges Da Siva minti na 13 da fara tamaula, sannan Ross Barkley ya ci na biyu a zagaye na biyu

Wannan ne karo na biyu ajere da aka doke Liverpool, bayan 3-0 da Watford ta yi nasara a kanta a gasar Premier a karshen mako.

Liverpool ta yi sauyin 'yan wasa bakwai daga wadanda suka buga karawa da Watford ranar Asabar - bayan da ta yi wasan Premier 18 a jere ba a doke ta ba.

Kungiyoyin biyu sun kara a bana sau biyu, inda suka yi 2-2 a European Super Cup ranar 14 ga watan Agustan 2019.

Sun kara haduwa a wasan Premier a Stamford Bridge ranar 22 ga watan Satumba, inda Liverpool ta yi nasara da ci 2-1.

Liverpool tana nan a matakinta na daya a kan teburin Premier da maki 79 da tazarar maki 22 tsakaninta da Manchester City mai biye da ita.

Asalin hoton, Getty Images

Ita kuwa Chelsea tana ta hudu a kan teburin Premier da maki 45 da tazarar maki 34 tsakaninta da Liverpool.

Chelsea za ta karbi bakuncin Everton a wasan gaba a gasar Premier, sannan ta ziyarci Aston Villa, sai kuma ta ziyarci Bayern Munich a gasar Champions League wasa na biyu ranar 18 ga watan Maris.

Liverpool kuwa za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasanta na Premier na gaba, sannan ta fafata da Atletico Madrid a wasa na biyu a Champions League.

Atletico Madrid ta doke Liverpool da ci 1-0 ranar 18 ga watan Fabrairu a Spaniya.

Asalin hoton, BBC Sport