Effiong da Israel na gaba a cin kwallo a Firimiyar Najeriya

Nigerian Premier

Asalin hoton, NPFL

'Yan wasa biyu ne ke kan gaba a yawan cin kwallaye a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya, bayan kammala wasannin mako na 22.

Kawo yanzu Ndifreke Effiomg na Akwa United da Israel Abia na Rangers kowanne ya ci kwallo goma-goma.

Victor Mbaoma na Enyimba International shi ne na biyu, wanda ya zura guda tara a raga a kakar ta Firimiyar Nigeria.

'Yan wasa biyu ne da suka ci kwallo takwas-takwas da ya hada da Tasiu Lawal na Katsina United da Ibrahin Mustapha na Plateau United.

Kwallo 20 aka zura a raga a ranar Lahadi da aka kammala wasannin mako na 22 da yi gumurzu tara a ranar.

Kuma wasa biyu ne kungiyoyin waje suka je suka samo maki uku a ranar ciki har da wanda Lobi Stars ta je ta doke Kwara United da ci 1-0.

Na biyun kuwa shi ne wanda Rivers United ta yi nasara a gidan Heartland da ci 2-0.

Kawo yanzu Plateau United ce ke kan gaba a teburin Firimiyar Najeriya da maki 40.

Sai Rivers United ta biyu da maki 39, Lobi Stars ma maki 39 ne da ita a matsayi na uku a teburin.

Wadanda suke 'yan kasan teburi kuwa sun hada da Nasarawa United da Kwara United da Jigawa Golden Stars, sai Adamawa United ta karshe ta 20.