Ivory Coast ta nada Beaumelle sabon kocinta

Ivory Coast

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast ta nada Patrice Beaumelle a matsayin sabon kocinta.

Mai shekara 41 ya maye gurbin Ibrahim Kamara, wanda ya bar aikin a cikin watan Fabrairu.

Karo na biyu kenan dan Faransa, Beaumelle zai yi aiki da Ivory Coast, bayan da ya yi mataimakin Herve Renard a lokacin da kasar ta lashe kofin nahiyar Afirka a 2015.

Ya kuma yi aiki da Renard a mataimakins a lokacin da ya horas da Zambia wadda ya lashe kofin nahiyar Afirka a 2012 da ita.

Kafin ya yi mataimakin Renard a Ivory Coast ya yi kocin Chipolopolo na wata tara.

Ya kuma yi aiki da Renard a Lille ta Faransa, bayan sun horas da Ivory Coast da kuma Saudi Arabia da Morocco.

Kalubalen farko da zai fara shi ne kai Ivory Coast gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2021 da wasan da zai yi na neman gurbin shiga gasar da Madagascar a karshen watan Maris.

Ivory Coast ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar da Masar ta karbi bakunci a 2019, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Aljeriya a bugun fenariti.