Harry Kane ya ce zai buga wa Ingila Euro 2020

Euro 2020

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan tawagar kwallon kafar Ingila, Harry Kane ya ce yana fatan zai warke kan a fara gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro 2020.

Rabon da dan kwallon mai shekara 26 ya taka leda tun 1 ga watan Janairu, inda ya karya kafa a karawa da Southampton.

Tun farko an yi tsoron cewar Kane ba zai warke kan gasar cin kofin nahiyar Turai ba, wacce za a fara ranar 12 ga watan Yuni, amma dan kwallon ya ce zai dawo atisaye a watan gobe.

Kane ya kara da cewar ''Idan dai ba wani abin ne gagarumi ya taso ba, zan halarci Euro 2020 da za a yi.''

Dan wasan wanda shekara biyar yana zama na daya a cin kwallo a Tottenham ya fara atisaye mai dan sauki shi kadai, tun kan ranar da aka sa ran zai KOMA fili.

Sai dai kuma ba zai yi wa tawagar Ingila wasan sada zumunta da za ta yi a gida da Italiya da Denmark ba a cikin watan nan.

Kane shi ne kan gaba a zura kwallaye a raga a gasar cin kofin duniya da aka yi a 2018 a Rasha, wanda Ingila ta kai wasan daf da karshe.

Shi ne na shida a jerin 'yan wasan Ingila da ke kan gaba a ci mata kwallaye, wanda yake da 32 a wasa 45 da ya yi mata.

Wasan farko da Ingila za ta buga a Euro 2020 shi ne da Croatia a Wembley ranar 14 ga watan Yuni.