Norwich ta yi fatali da Tottenham daga FA Cup

Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham ta yi ban kwana da gasar FA Cup a zagaye na biyar, bayan da Norwich City ta doke ta a bugun fenariti.

Tun farko kungiyoyin sun buga 1-1 har da karin lokaci, daga nan ne aka je bugun fenaritin.

Jan Vertonghen ne ya fara ci wa Tottenham kwallo minti 13 da fara tamaula, inda Norwich ta farke saura minti saura minti 12 ta hannun Josip Drmic.

A bugun fenaritin ne Norwich ta yi nasara da ci 3-2 ta kuma kai wasan daf da na kusa da na karshe.

Mai rike da kofin Manchester City ta kai Quarter Finals, bayan da ta ci Sheffield Wednesday 1-0, kuma Sergio Aguero ne ya ci mata kwallon.

Leicester City ma ta kai zagayen gaba, bayan da ta yi nasara a kan Birmigham da ci 1-0.

Ricardo Pereira ne ya ci wa Leicester kwallon da ya kai ta karawar da fa da na kusa da na karshe.

Tottenham da Norwich City sun buga Premier karo biyu a bana, inda ranar 28 ga watan Disamba suka yi 2-2 a gidan Norwich.

A wasa na biyu kuwa Tottenham ce ta yi nasara a kan Norwich da ci 2-1 ranar 22 ga watan Janairu.

Tottenham tana ta bakwai a kan teburin Premier da maki 40, ita kuwa Norwich ita ce ta karshe ta 20 da maki 21.